Now livetag icon
NEW REPORT: Knowing your true competitive position across Web & AppDownload Reportbanner icon

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar 앱 분석 (10월 6일)

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar

  • Abdulkarim Nasir
  • Apple App Store
  • 유료
  • 교육
Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 - Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Download this app to learn how to pray the Muslim Prayer as taught by Prophet Muhammad (s.a.w). The audio is in Hausa language and works perfectly offline. You can also follow the lessons by reading the sift Salah an-nabi in Arabic text Siffatus Salatin Nabi mp3 da pdf karatun littafin (Sifat Salat Nabiy Hausa) a inda mawallafin littafin Muhammad Nasiruddeen Al Albani yayi bayanin yadda sallar manzon Allah (s.a.w) take tun daga kabbarar-harama har zuwa sallama kamar kana Kallon Annabi yanayin sallar. Fassarar littafin da darusan na marigayi mallam Jafar Mahmud Adam ne. Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 Offline Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam agarin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, awurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi nemu sabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano. Tun kafin zuwansu Kano, marigayi Sheikh Ja'afar yariga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan. Kafin rasuwarsa, ya riga yayi nisa wajen karatunsa na digiri na 3, wato digirin digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa. Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar dasu, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy. Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre). Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da aka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi. Ya bar mata 2, da 'yaya 6, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa. Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan aljanna.
Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar

스토어 순위

스토어 순위는 Google과 Apple이 설정한 여러 매개변수를 기반으로 합니다.

모든 카테고리 ·
미국--
교육 ·
미국--
월평균 다운로드를 확인하려면 계정을 만드세요문의하기

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar 순위 통계 추이

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar의 Similarweb 사용량 순위 및 Apple App Store 순위

순위

데이터가 없습니다

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar 국가별 순위

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar의 주요 카테고리 순위가 가장 높은 국가입니다


주요 경쟁 앱 및 대체 앱

같은 스토어에서 동일한 사용자가 사용할 가능성이 높은 앱입니다.

MA'ANONI DA SHIRIYAR ALQUR'ANI

MA'ANONI DA SHIRIYAR ALQUR'ANI

Essa Naser A Duraibi

DuaApp

DuaApp

Abdi Sheikh

Darulfikr Pro

Darulfikr Pro

Basheer Ridwan Muhammad

Hausa Quran

Hausa Quran

RAVINDHIRAN SUMITHRA

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar VS.

10월 6, 2026